'Najeriya za ta lashe gasar kwallon nahiyoyi'

Tawagar Super Eagles ta Najeriya
Image caption Tawagar Super Eagles ta Najeriya

Manajan kungiyar kwallon kafa na Najeriya, Steven Keshi ya ce kasar na da niyyar daukar kofin gasar kwallon kafa na nahiyoyi, idan ta je Barazil a watan Yuni mai zuwa.

Najeriya ta lashe gasar zakarun kwallon kafa na nahiyar Afrika ne, bayan ta doke Burkina Faso da ci daya mai ban haushi.

Hakan kuma yasa kasar ta samu tikitin shiga gasar nahiyoyin duniya a karo na farko.

Keshi ya shaida wa BBC cewa " Zamu je Brazil ba wai saboda yawon bude ido ba, amma domin mu dauki kofi."

Najeriya zata fuskanci Tahiti da Uraguay da Spaniya a Brazil, kasar da zata yi amfani da damar gasar wajen daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2014.

A gasar nahiyoyin, Najeriya zata taka leda ne a rukunin B, yayin da mai masaukin baki Brazil kuma, za ta kara da Italiya da Mexico da kuma Japan a rukunin A.

An fara gasar cin kofin nahiyoyin ne a shekarar 1992, kuma ana yin ta ne duk bayan shekaru hudu.

Haka kuma tun fara gasar ta nahiyoyin babu kasar Afrika da ta taba daukar kofi, kodayake Kamaru ta zo ta biyu a gasar da aka yi a shekarar 2003.

Sai dai Keshi na da kwarin guiwar cewa, tawagar Najeriya da ta lashe kambun Afrika a karo na uku, zata kai ga daukar kofin gasar nahiyoyin.

Karin bayani