Zakarun Turai : PSG ta ci Valencia

'yan wasan psg
Image caption Paris St-Germain ta bi Valencia gida ta doke ta

Kungiyar Paris St-Germain ta Faransa ta sami nasara a kan Valencia da ci 2-1, a karawar farko ta kungiyoyi 16 ta cin Kofin Zakarun Turai.

Ezequiel Lavezzi ne ya fara ci wa PSG kwallonta bayan minti goma da fara wasa.

Javier Pastore ya biyo baya da kwallo ta biyu a minti na arbain da uku a na shirin tafiya hutun rabin lokaci.

Sai dai a na dab da tashi daga wasan a minti na casa'in ne masu masaukin bakin wato Valencia su ka sami nasarar rama kwallo daya ta hannun Rami.

A farkon watan Maris za a yi karawa ta biyu a Paris.