Olympics : An cire wasan kokawa

'yan kokawa
Image caption 'Yan kokawar wrestling ba za su shiga olympics ba kuma

Kwamitin wasannin Olympics na Duniya ya fitar da wasan kokawar turawa daga jerin wasannin gasar ta 2020 domin maye gurbinsa da wani sabon wasan.

'yan kwamitin sun yanke shawarar daukar matakin ne bayan sun duba yadda aka gudanar da dukkanin wasanni 26 da aka yi a gasar Olympics ta Landan.

Sai dai kuma kakakin hukumar ta Olympics Mark Adams ya ce wannan ba shi ne hukunci na karshe ba a kan cire kokawar ta wrestling daga jerin wasannin ya ce shawara ce dai kawai.

Kakakin ya ce ''ba wai magana ce a kan abun da ba shi da kyau ba ne game da wasan na kokawar wrestling illa dai abun da ya fi dacewa da gasar ta Olympics ne kawai.

Ana ganin dai da wuya a sake dawo wa da wasan na kokawa domin a kwai wasu wasannin guda bakwai da za a duba a ga wanda ya fi dacewa a sa a cikin jerin wasannin gasar 26.

Karin bayani