Kurket: An fitar da kungiyar mata ta Ingila

Kungiyar wasan kurket ta mata ta Ingila
Image caption Kungiyar wasan kurket ta mata ta Ingila

A cigaba da gasar cin kofin duniya na kurket da ake yi a Mumbai, an fitar da kungiyar mata ta Ingila, bayan West Indies ta doke Australia.

Hakan ne ya sa West Indies ta samu zuwa zagayen karshe na gasar da ake yi a India.

Da ace an doke West Indies a karawarsu da Australia, da hakan ya baiwa Ingila damar shiga zagayen karshe saboda doke New Zealand da ta yi a ranar Laraba.

Wannan ne karon farko da West Indies ta samu zuwa zagayen karshe a gasar.

A karawar farko a lokacin da aka bude gasar, India ta doke West Indies, sai dai daga bisani, India bata samu cancantar shiga gasar ba.