FIFA ta raba rigimar Drogba

didier drogba
Image caption Didier Drogba ya tabbata dan wasan Galatasaray

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta baiwa Didier Drogba damar buga wasa a kungiyar Galatasaray ta Turkiyya.

FIFA ta ba shi izinin ne duk da dagewar da kungiyar Shanghai Shenhua ta China ta yi cewa har yanzu dan wasanta ne.

A watan da ya gabata ne dan wasan na Ivory Coast ya kulla yarjejeniyar komawa klub din na Galatasaray, zakarun Turkiyya.

Wakilin dan wasan ya ce Drogba ya na da damar komawa wata kungiya saboda rashin biyansa albashi da klub din na China ba ya yi.

A makon da ya wuce ne Drogba ya sami gagarumar tarba a Istanbul daga magoya bayan kungiyar ta Galatasaray kuma a ka binciki lafiyarsa ranar Litinin a Kungiyar.

Karin bayani