Man U ta kwaci kunnen doki a Madrid

manchester united da real madrid
Image caption Welbeck ya jefa kwallo ragar Real Madrid

Manchester United ta bi Real Madrid har gida ta yi kunnen doki da ita 1-1 a gasar Zakarun Turai.

Danny Welbeck ne ya fara jefa kwallo a ragar Real Madrid a minti na 20 da fara wasa.

Minti goma tsakani kuma sai Cristiano Ronaldo ya rama kwallon.

Wannan ita ce karawar farko tsakanin kungiyoyin biyu a zagayen kungiyoyi 16 na gasar.

Da wannan sakamako na kwallon da Manchester United ta ci a gidan Real Madrid din ta na sa ran samun dama a kan 'yan Madrid din a karawar da za su yi ta biyu ranar 5 ga watan Maris a Old Trafford.