Zakarun Turai :Shaktar da Borussia 2-2

mats hummels
Image caption Mats Hummels ya ramawa Borussia kwallo ta biyu

Kungiyar Shaktar Donetsk ta Ukrain ta tashi canjaras 2-2 da Borussia Dortmund ta Jamus a Ukrain.

Wannan ita ce karawar farko ta matakin kungiyoyi 16 na gasar cin Kofin Zakarun Turan.

Darijo Srna ne ya fara ciwa Shaktar kwallonta a minti na 31.

Amma minti goma tsakani sai Robert Lewandowski ya ramawa Jamusawan.

Can kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sai a minti na 68 Douglas Costa ya sake jefa kwallo ta biyu a ragar bakin.

Ana saura minti uku wa'adin wasan ya cika na minti 90 sai Hummels ya rama ta biyu.

Sai kuma karawa ta biyu da kungiyoyin za su yi a Jamus a watan Maris