Ferguson :Van Persie ya kusa da Messi da Ronaldo

robin van persie
Image caption Van Persie ya ci wa Manchester United kwallaye 23

Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce dan wasan kungiyar Robin van Persie ya na hanyar zama mataki daya da Cristiano da Messi.

Ya ce dan wasan mai shekaru 29 ya na hanyar cimma matakin da za a iya kwatanta shi da gwanayen 'yan wasan biyu.

Ferguson ya ce zuwan Van Persie Manchester United kwalliya na biyan kudin sabulu.

Ya zuwa yanzu Van Persie ya ci wa Manchester United kwallaye 23 tun lokacin da Arsenal ta sayar da shi a kan fam miliyan 24 a watan Agusta.

Haka kuma game da Cristiano Ronaldo, Ferguson ya ce yanzu ya fi yadda yake a da sabo da ya girma.

Ya ce ''Cristiano ya na kan ganiyarsa yanzu, kuma zai ci gaba da kasancewa haka nan da shekaru uku ma su zuwa.''