Qatar Open : Azarenka ta yi galaba

victoria azarenka
Image caption Victoria Azarenka ta daya a duniya

Victoria Azarenka ta sami nasara a kan Romina Oprandi 'yar Switzerland a gasar wasan tennis ta Qatar Open da maki 6-2 6-3.

Da wannan nasara ta samu zuwa zagaye na uku na gasar inda za ta fafata da Christina McHale 'yar Amurka wadda iat ce ta ke matsayi na 44 na gwanayen wasan tennis a duniya.

Azarenka ta daya a duniya wadda kuma ke rike da kofin gasar ta dawo fagen wasan ne bayan ta sami nasarar gasar Australian Open.

Yanzu dai kwararrun 'yan wasan tennis din mata su na fafutukar samun matsayi na daya a duniya.

Idan Serena Williams ta kai matakin wasan kusa da na karshe a gasar da ake yi a Dohan za ta sami matsayin.

Amma kuma Azarenka za ta ci gaba da rike matsayin ta dayan idan ta kai wasan karshe kuma Serena ta kasa kaiwa wasan kusa da na karshen.

Ita kuma Maria Sharapova za ta sake karbar matsayin ta daya a duniyar ne idan ta dauki kofin gasar ta Qatar Open, wato idan har Serena Williams ta kasa zuwa wasan kusa da na karshen Azarenka kuma ta gaza kaiwa wasan karshe.

To a halin da ake ciki Serena williams ta tsallake zuwa wasan gab da na kusa da karshe a gasar bayan ta buge Urszula Radwanska da maki 6-0 6-3.

A ranar Juma'a Williams 'yar shekara 31 za ta kara da Petra Kvitova.

Ita kuwa Sharapova ta kai zagayen na gaba ne da maki 6-3 6-3 da ta samu a kan Klara Zakopalova 'yar czech kuma za ta kara a gaba da Stosur 'yar Australiya.

Can a Rotterdam kuwa na biyu a fagen wasan tennis din a duniya Roger Federer ya murkushe Grega Zemlja dan Slovenia da maki 6-3 6-1 a cikin mintuna 57 kacal.