Oscar Pistorius 'ya harbe budurwarsa'

Oscar da budurwarsa Reeva
Image caption An harbi Reeva a ka da kuma kirji, ta mutu a gidan Oscar dake Pretoria, kafin a kaita asibiti

An kama zakaran tseren nakasassu na kasar Afrika ta Kudu Oscar Pistorius ya harbe budurwarsa a gidansa dake Pretoria, a cewar kafar yada labarai ta kasar.

'Yan sanda sun yi awon gaba da Mr Pistorius a game da lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Haka kuma sun damke wani wani mutum, da basu bayyana sunansa ba, mai shekaru 26, yayin da suka fara bincike game da kisan.

Yanayin da ya kai ga mutuwar budurwar na da sarkakiya, sai dai rahotanni na cewa watakila ya harbe ta ne, saboda daukar cewa barawo ne.

Mista Pistorius mai shekaru 26 shi ne mutum na farko da bashi da kafafuwa biyu, da ya fara tsere a gasar Olympics.

Nan gaba kadan ne, ake sa ran za a gurfanar da shi a gaban kuliya.

Kafafen yada labarai na kasar sun bayyana sunan budurwar da cewa, wata mai tallar kayan kawa ce mai suna Reeva Steenkamp.