Kofin FA : Chelsea ta yi nasara

chelsea da brentford
Image caption Chelsea ta lallasa Brentford

Chelsea ta sami damar zuwa zagaye na gaba na gasar cin Kofin Kalubale na Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA bayan ta yi galaba a kan Brentford da ci 4-0.

Juan Mata ya fara ci wa Chelsea mai rike da Kofin kwallonta a minti na 54 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Sai kuma Oscar wanda a minti na 68 ya ci kwallo ta biyu kafin Frank Lampard ya kafa tarihi a kungiyar ta Chelsea da kwallo ta uku a minti na 71.

Kwallon ta Lampard ita ce ta 26 a gasar cin Kofin FA da ya ci wa kungiyar wadda kuma ta bashi damar zama dan wasan da ya fi kowanne dan wasanta cin kwallo a gasar, har ma ya wuce Bobby Tambling.

Haka kuma kwallon ita ce ta 199 da dan wasan ya ci wa Chelsea jumulla.

A minti na 81 ne kuma John Terry ya jefa kwallo ta hudu kuma ta karshe a ragar Brentford wadda ta kara tabbatar wa Chelsean zuwanta gidan Middlesbrough ranar 27 ga watan Fabrairu domin haduwa.

A karawar farko dai a gidan Brentford wadda ta ke kasa da gasar Premier wato League One an tashi ne 2-2.

Karin bayani