Arsenal za ta binciki lafiyar Koscielny

'yan wasan arsenal
Image caption Arsenal za ta kara da Munich ba bu wasu 'yan wasan

Ya yin da Arsenal ke shirin karawa da Bayern Munich ranar Talata a gasar Kofin Zakaraun Turai zagayen kungiyoyi 16 za ta duba lafiyar dan wasanta Laurent Koscienly wanda ke ciwon guiwa.

Sauran 'yan wasan na Arsenal da ba za su buga wasan ba su ne dan wasan baya Nacho Monreal da Kieran Gibbs wanda ya ji rauni a cinya amma kuma Carl Jenkinson shi ma dan wasan baya ya dawo wasa bayan an dakatar da shi wasa daya.

Ita ma Kungiyar Bayern Munich wadda ke kan gaba a gasar lig din Jamus har yanzu dan wasansu na gaba Claudio Pizzaro bai dawo wasa ba saboda rashin lafiya da Holger Badstuber shi ma.

Haka kuma Jerome Boateng shi ma ba zai buga wasan na Talata ba saboda dakatar da shi da aka yi, sai dai kuma dan wasanta na tsakiya Javi Martinez zai buga saboda ya samu lafiya.

Kocin na Bayern Jupp Heynckes ya gargadi 'yan wasansa da kada rashin nasarar da Arsenal ta yi ta Kofin FA a hannun Blackburn ta sa su raina klub din. Ya ce '' duk da wannan sakamako Arsenal ta samu kanta a 'yan makwannin da su ka wuce; su na da 'yan wasa masu kyau.''