Mancini : Ni ne na daya a Ingila

roberto mancini
Image caption Roberto Mancini, ''ba bu gwani kamata a Ingila''

Kocin Kungiyar Manchester City Roberto Mancini ya ce yanzu a duk Ingila babu wani gwanin mai horadda 'yan wasa kamarsa kuma ba ya fuskankar barazanar kora daga aikinsa.

Kocin ya na wannan ikirarin ne kuwa duk da cewa an fitar da Kungiyarsa daga gasar cin Kofin Zakarun Turai kuma ta na tsaka maiwuya ta kare kofin Premier da ta ke rike da shi.

A yanzu babbar abokiyar hamayyarta Manchester United ta na gabanta da maki goma sha biyu a gasar ta Premier.

Duk da cewa City din ta samu nasarar zuwa matakin wasan gab da na kusa da karshe na cin Kofin Kalubale na Hukumar Kwallon Kafa ta Ingila, FA, tsohon dan wasan kungiyar Danny Mills ya ce yana ganin akwai bukatar sauya kocin a karshen kakar bana.

A tsawon lokacin da ya kama aiki a klub din Mancini ya jagoranci kungiyar zuwa matsayi na uku a Premier kuma ta sami damar shiga gasar Zakarun Turai.

A bara Manchester City ta samu nasarar cike ratar maki 12 tsakaninta da Manchester United har ta dauki Kofinta na Premier na farko bayan ta ci QPR 3-2.

Bayan da Man City ta yi nasara a kan Leeds da ci 4-0 ranar Lahadi, Mancini ya yi kurari da shaguben cewa '' a tsawon watanni shida wani ya ce Manchester City za ta sauya kociya, za ta kawo Guardiola, kuma bayan Guardiola ya tafi Bayern Munich, yanzu kuma wani kocin zai zo.

''Na dauki Kofin Premier daya da Kofin Kalubale na FA da na Charity, ba bu wani kociya da ya yi nasara kama ta a watanni 15 da su ka gabata.''

Karin bayani