Serena Williams ta shiga tarihi

serena da azarenka
Image caption Azarenka ta kawo karshen galabar da Serena ke yi a kanta

Serena Williams ta zama mace mafi yawan shekaru da ta zama ta daya a wasan tennis a duniya.

Williams wadda ta cimma wannan matsayi da shekaru 31 da kwanaki 145 ta karbe matsayi na daya a tennis a duniya daga Victoria Azarenka.

Ta dawo matsayin ta dayan ne bayan da ta je wasan kusa da na karshe na gasar Qatar Open.

Duk da cewa Azarenka ta buge ta a wasan karshe Williams ta samu isasshen makin da ya ya sa ta karbe matsayin daga Azarenka 'yar kasar Belarus.

Ita kuwa Azarenka da nasarar da ta samu da maki 7-6 2-6 6-3 ta kawo karshen galabar da Serena ke yi har sau tara a jere kanta.

Serena ta rike matsayin ta daya a duniya a wasan na tennis a watan oktoba na 2010 kafin ta gamu da ciwon kafa.

'yar tennis din ta kuma maye gurbin 'yar uwarta ba Amurkiya Chris Evert a matsayin mace mafi yawan shekaru da ta zama ta daya a fagen tennis din a duniya. Evert ta rike matsayin ne a 1985 kafin ta kai shekara 31.