China ta ci tarar kulob din Shenhua

Magoya bayan kulob din Shenhua na rike da hoton drogba
Image caption Magoya bayan kulob din Shenhua na rike da hoton Drogba

Hukumar kwallon kafa ta Sin ta kwace kofin da kulob din Shanghai Shenhua ya samu, na gasar zakaru a shekarar 2003, saboda cogen wasa.

Sannan hukumar ta ci tarar kulob din dalar Amurka dubu 160, a cigaba da sanya takunkumi game da abubuwan da suka shafi cin hanci da rashawa.

A bara ne kulob din ya dauki dan wasan Ivory Coast din nan, Didier Drogba na wani dan gajeren lokaci, domin farfado da kulob din.

An samu kulob din da laifin sayar da wani wasa, kafin su kai ga daukar kofin gasar.

A yunkurin da kasar take na tsaftace harkar wasan kwallon kafa, an ci tarar wasu kulob-kulob din tare da rage musu maki.

Yayin da 'yan wasa da jami'ai fiye da talatin kuma, aka haramta musu wasa a fadin rayuwarsu, wasu kuma aka daure su saboda cin hanci da rashawa.