FIFA ta amince da fasahar cin kwallo

sepp blatter
Image caption Sepp Blatter ya matsa a yi amfani da fasaha

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta amince da amfani da fasahar tabbatar da shigar kwallo a raga a gasar cin Kofin Duniya ta 2014 da za a yi a Brazil.

Haka kuma Hukumar ta amince a yi amfani da tsarin a gasar cin Kofin Zakarun Nahiyoyi ta 2013 a Brazil.

An samu nasarar jarraba fasahar a gasar cin Kofin Duniya na Kungiyoyi da aka yi a Japan a watan Disamba na 2012.

Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Sepp Blatter ya kafe a kan bukatar amfani da tsarin wanda za a sanya na'urorin daukar hoto a raga da kuma wata naura mai kurar karfe da zasu rika tantance shigar kwallon raga.

Blatter ya matsa a aiwatar da tsarin tun lokacin da yaga yadda alkalin wasa ya hana kwallon da Frank Lampard na Ingila ya ci Jamus a gasar Kofin Duniya na 2010, karawar da Jamus ta yi nasara.

Haka kuma shugaban ya kara tabbatar da bukatar amfani da fasahar a wasan kwallon kafa bayan ce-ce-ku-cen da aka yi a kan nasarar da Ingila ta yi a kan Ukraine a wasan Kofin Kasashen Turai na 2012 inda alkalin wasa ya ki amincewa da kwallon da Ukraine ta jefa a ragar Ingila.