AC Milan ta ce ba za a lallasa ta ba

ac milan barcelona
Image caption Karon battar AC MIlan da Barcelona

Kocin AC Milan ya ce ba kamar yadda kowa ya ke dauka ba ba za ayi musu kaca-kaca ba idan suka hadu da Barcelona a karawarsu ta cin Kofin Zakarun Turai.

Massimiliano Allegri ya ce ''mun san cewa za mu hadu ne da kungiyar da tafi kowace kungiya a duniya amma ba zan yarda cewa za a lallasa mu ba.''

Milan wadda ta fara kakar wasan bana tana tangal-tangal ta farfado har ta kai matsayi na 4 a gasar Serie A ta lig din Italiyan.

Barcelona kuwa a yanzu ita ce ta daya da maki 12 a lig din Spaniya da take kan hanyar karbe kofin daga abiyar hamayyarta Real Madrid.

Mataimakin kocin Barcelona Jordi Roura wanda ke jagorantar klub din a wannan karawa yayin da ake yiwa kocin Tito Vilanova maganin ciwon dajin da yake fama da shi ya ce ba kungiyarsu ce za a ce zata yi nasara ba.

Yace idan manyan kungiyoyi suka hadu a wannan mataki ba za a ce wata ta fi wata ba .

Roura ya ce muna mutunta Milan sosai wadda ta fi kowa daukar kofin na zakarun Turai.

Ita dai AC Milan sau 7 tana daukar Kofin na Zakarun Turai, yayin da Barcelona ta dauka sau 4.

Barcelona ba ta taba rashin nasara a haduwarta da AC Milan din ba. A karawarsu a bara a gasar ta Kofin sun yi canjaras sau biyu a wasan rukuni, a wasan gab da na kusa da karshe kuwa Barcan ta yi galaba sau biyu.

Karin bayani