Wilshere ya ce kada a ga laifin Wenger

  • 20 Fabrairu 2013
Jack Wilshere
Image caption Jack Wilshere

Dan wasan tsakiya na kulob din Arsenal, Jack Wilshere ya ce, kada a dora wa manajan kulob din laifi game da gazawar su na daukar kofi, laifin na 'yan wasa ne.

Gunners sun yi fatan kaiwa ga wasan gaf da na kusa da na karshe a gasar Champions league, amma Bayern Munich ta doke su da ci uku da daya, a taka ledar da suka yi a filin wasa na Emirates.

Haka kuma a ranar Asabar data gabatane, kulob din ya sha kaye a hannun Blackburn da ci daya da nema.

Wilshere ya ce " Manajan ya ja ragamar kulob din na tsawon shekaru 16, kuma ya yi nasa kokarin, saboda haka ba za a dora masa laifi ba."

Arsenal dai ita ce ta biyar a gasar Premier League, kuma Tottenham wacce ke da dama ta karshe ta shiga gasar Champions League, ta dara Arsenal da maki hudu.

Samun shiga gasar Chmapions League shi ne fatan da Gunners ke da shi kadai, na daukar kofi a wannan kakar wasannin.

Kulob din na bayan Manchester United da maki 21, kuma gashi an kori Arsenal din daga gasar Capital Cup one.