Man U : Gill zai sauka daga shugabanci

david gill
Image caption Ferguson bai ji dadin saukar David Gill ba

Kungiyar Manchester United ta tabbatar cewa David Gill zai sauka daga shugabancinta a ranar 30 ga watan Yuni.

Sa dai Gill dan shekara 55 wanda ya fara aiki da klub din a watan Fabrairu na 1997 a matsayin darektan kudi kafin ya zama shugaba a 2003 zai ci gaba da zama a matsayin darekta a kungiyar.

Mataimakinsa Ed Woodward shi ne zai dare kujerarsa.

Gill ya ce matakin da ya dauka na sauka daga shugabancin da maye gurbinsa da Woodward zai taimaka wajen sabunta klub din kamar yadda ya ambata.

Kocin kungiyar Sir Alex Ferguson bai ji dadin shawarar da Gill din ya yanke ba ta ajiye mukamin nasa.

Ya ce ''babbar asara ce a wurina amma tun da zai ci gaba da zama a hukumar kungiyar hakan zai karfafa min guiwa.''

Sir Alex ya kara da cewa ''idan da zan iya shawo kansa ya sauya shawara da sai na yi, to amma ya riga ya yanke hukunci kuma ina mutunta shi a kan hakan.''

A karkashin shugabancin Gill din ribar da Manchester United ta ke samu ta karu zuwa kashi 74 cikin dari a watanni shidan karshe na 2012.

Amma kuma ana bin klub din bashin fam miliyan 366.6 kuma kudaden da a ke kashewa 'yan wasa da ma'aikata ya karu da sama da kashi 10 cikin dari.