Barcelona za ta yi wasa don hadakai

lionel messi
Image caption Ana saran Lionel Messi zai yi wasan

Shugaban kasar Isra'ila da shugaban Kulab din Barcelona sun bayyana cewa suna shirya wani wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta hadin-gwiwa tsakanin yahudawa da Palasdinawa da kuma Barcelona

Za a kara ne a karshen watan Yuli a dandalin Ramat Gan da ke Isra'ila.

Irin kauna da goyon bayan da ake yi wa Barcelona suka sa hada kan Palasdinawa da Yahudawa magoya bayan kulab din da ke bangarori biyun da ke fada da juna.

Shugaban kulab din wanda ke wata ziyara a Isra'ila da kuma gabar yammacin kogin Jordan a karon farko ya bayyana cewa kulab din na so ya yaukaka dankon zumunci tare da wanzar da zaman lafiya da lumana a yankin ta hanyar wasan kwallon kafa.

Ba a dai san ko su wa da wa za a ayyana sunayensu a matsayin wadanda za su taka ledar ba, amma ana sa ran manyan 'yan wasan Palasdinawa da yahudawa ne za su shiga wasan, inda za su kara da 'yan Barcelonan.

Ana dai sa ran gwarzon na 'yan wasan kwallon kafa Lionel Messi na daga cikin wadanda za su kai ziyara can.

A bara dai harkar siyasar Gabas-ta-tsakiya ta shafi kulab din na Barcelona.

Saboda ta karrama wani tsohon sojan kasar Isra'ila, Gilad Shalit, wanda masu fafitikar Palasdinawa suka tsare shi shekara biyar ta hanyar gayyatarsa a matsayin bako na musamman don ya kalli wasan da ta yi da Real Madrid, a Nuo Camp.

Wannan ya bata wa Palasdinawa rai, amma daga baya Kungiyar Barcan ta gayyaci wani tsohon dan wasan kwallon kafa a yankin Palasdinawa, wanda kasar Isra'ila ta tsare tsawon shekara uku a matsayin bako na musamman zuwa kallon wani wasanta, amma bai amsa gayyatar ba.

Karin bayani