An damke wanda ake zargi da cacar kwallo

Shugaban hukumar 'yan sandan kasa da kasa Ronald Noble
Image caption Shugaban hukumar 'yan sandan kasa da kasa Ronald Noble

Wani da ake zargi da hannu wajen cogen wasan kwallon kafa na kasa da kasa ya shiga hannun jami'an tsaro a Italiya.

An damke shi ne a lokacin da ya isa Italiya daga Singapore, inda ya mika kansa ga 'yan sanda.

Kafofin yada labaran Italiya sun bayyana sunan mutumin da Admir Sulic.

Hukumar 'yan sanda ta kasa da kasa tace an yi imanin cewa, wanda ake zargin yana da alaka da wata kungiya dake hada cogen wasan kwallo dake Singapore.

Hukumar ta yi imanin cewa Mr. Sulic na da alaka da kungiyar cogen wasan kwallon, wanda wani dan kasuwan Singapore Tan Seet Eng da aka fi sani da Dan Tan ke da ita.

Masu bincike dai na sukar Singapore game da abin da suka kira, barin mai cacar wasanni ya zauna a kasar, ba tare da wata tsangwama ba.

Rahotannin fari dai sun nuna cewa shi ma Mr. Tan yana cikin jirgin da ya taho daga Singapore ya sauka a Italiyan.