Bana tunanin ajiye aiki- Wenger

Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce bai taba tunanin ajiye aikinsa ba a wannan mako.

Arsenal dai na fuskantar kalubalen kaiwa wasan dab da kusa da na karshe a gasar zakarun Turai bayan ta sha kashi a hannun Bayern Munich a wasan kifa daya kwalla da aka yi a ranar Talata.

Kashin da ta sha a hannu Bayern din ya biyo bayan fidda ta da aka yi a gasar cin kofin FA.

"Ya kamata mu hada kai, kada mu bari korofen korofen mutanen su karya lagwan mu saboda wasa daya." In ji Wenger.

Wenger dai ya fuskancin matsin lamba a wannan makon a yayinda wasu rahotanni ke nuni da cewa yana tunanin ajiye aikinsa.

Arsenal dai ba ta lashe kofi ba tun baya da ta doke Manchester United a bugun fenarity a gasar cin kofin FA a shekarar 2005.

A wani taron manema labarai da aka yi, an tambayi Wenger ko zai ajiye aikinsa, sai ya maida martani da cewa; "ko kadan bana tunanin hakan".

"Ina da kwantaragi har zuwa shekara 2014 kuma muna cikin wani dan gejeren lokaci ne yanzu. Sai shekara ta 2014 zan yi tunani abun da zan yi idan kwantaragi na ya kare".