Cazorla ya taimakawa Arsenal a wasa da Villa

Arsenal ta dan samu sa'ida bayan nasarar da ta yi a kan Aston Villa da ci biyu da daya.

Kungiyar dai ta dan fuskanci matsin lamba a makon da ya gabata saboda rashin nasarar da ta yi ta fuskanta.

Cazorla ne ya fara zura kwallon farko ana minti shida da fara wasan.

Amma daga bayan ta yi sakaci har sai da Andreas Weimann ya fanshewa Villa.

Sai dai ana sauran mintuna biyar ne a tashi wasan Cazorla ya kara sanya Arsenal a gaba.

A yanzu haka dai maki daya ne ya rage tsakanin Arsenal da Tottenham wadda ke mataki na hudu.