Sarkin kokawar Nijar ya sha kasa

Tutar Jamhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar, ranar Lahadi ake shiga rana ta biyu ta kwambalar kokawar gargajiya karo na talatin da hudu da ake yi a Yamai.

Kokawa biyu aka yi da bude kwambalar, kuma wacce ta fi bayar da mamaki ita ce wacce aka yi tsakanin Jihar Maradi da Jihar Agadas.

Tuni dai sarkin ’yan kokawa Laminu Mai Dabba na Agadas ya sha kasa—wani sabon jinni Abdour Rahman Sabiu ne ya kayar das hi—a karawar tsakanin Maradi da Agadas inda Maradin ta yi wa Agadas kaye tara da daya.

Karawa ta biyu ita ce tsakanin Damagaram da Tillaberi—Damagaram ta samu kaye shida, Tillaberi na da hudu.

Da maraca kuma a karawar Tahoua da Diffa an tashi biyar da biyar; sai kuma karawar Dosso da Yamai, wacce aka tashi Dosso na da kaye shida Yamai na da kaye hudu.

Daga cikin ’yan kokawa tamanin dai tuni arba’in suka fadi.

Ranar Lahadi akwai karawa tsakanin Agadas da Damagaram; sai kuma tsakanin Dosso da Tahoua.