Man City ta casa Chelsea 2-0

manchester city
Image caption Manchester City ta yukuro a Premier

Manchester City ta yunkuro a kokarin da ka te yi na ganin ta kamo Manchester United a gasar Premier inda ta yi nasara akan Chelsea 2-0.

Yaya Toure ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea a minti na 63 bayan sun yi ta barar da damar da suka samu.

Minti bakwai da dawo wa daga hutun rabin lokaci Chelsea ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida amma Frank Lampard ya kasa cin kwallon.

Maitsaron gidan Manchester City Joe Hart ya buge kwallon ne wadda da ta ci za ta zama ta 200 da Lampard din ya ci wa Chelsea.

Can a minti na 85 ne kuma Carlos Tevez ya ci wa Man City kwallo ta biyu.

Yanzu maki 12 ne tsakanin Manchester United ta daya a gasar ta Premier da abokan hamayyarta 'yan Manchester City na biyu.

Wannan shi ne karo na hudu a jere da Chelsea ta ke rashin nasara a Etihad (gidan Man City).

kuma ta na bin City a matsayi na uku da maki 7 a tsakaninsu ya yin da ya rage wasanni 11a kammala gasar ta bana.

Karin bayani