Newcastle ta ci Southampton

newcastle da southapton
Image caption Newcastle ta taso daga baya ta yi galaba

Newcastle ta farfado daga baya ta yi nasara akan Southampton wadanda dukkansu ke fuskantar faduwa daga gasar Premier.

Morgan Schneiderlin ne ya fara ci wa Southampton kwallo minti 31 da fara wasa, amma minti biyu tsakani Mousa Sissoko ya rama wa Newcastle.

Papis Cisse ya ci wa Masu masaukin bakin Newcastle kwallo ta biyu a minti na 42 amma kuma dai Rickie Lambert ya rama a minti na 50.

Yohan Cabaye ya sanya Newcastle a gaba da bugun fanareti a minti na 67.

A minti na 75 Hooivelt na Southampton ya ci kansu da kansu abin da ya baiwa Newcastle kwallo ta hudu.