Swansea ta dauki kofin Capital One

swansea da bradford
Image caption Swansea ka dauki kofinta na farko

Kungiyar Swansea ta dauki babban kofinta na farko bayan da ta lallasa Bradford ta League two 5-0 a Wembley.

Kofin Capital One shi ne wani babban kofi da Swansea ta dauka a tarihinta na shekara 111.

Kungiyar ta fara shige wa gaba ne bayan Nathan Dyer ya jefa kwallon da Michu ya bugo mai tsaron gidan Bradford ya kade a raga a minti 16 da fara wasa.

A minti na 40 ne kuma Michu shi ma ya ci ta biyu.

Dyer ya sake jefa kwallonsa ta biyu kuma ta ukun Swansea a minti na 47.

Jonathan De Guzman ya samu fanareti bayan da mai tsaron gidan Bradford Duke ya kayar da shi kuma alkalin wasa ya kore shi.

De Guzman ne ya buga fanaretin kuma ya ci a minti na 59, sannan kuma ana shirin tashi bayan mintuna 90 na wasan ya kara jefa wata kwallon raga ta biyar ke nan.

Swansea ta fitar da kungiyoyi uku na gasar Premier, Wigan da Arsenal da kuma Aston Villa kafin ta kai ga wannan nasara.