Wenger : Arsenal za ta iya zama ta biyu

arsene wenger
Image caption Arsene Wenger na sa rai da matsayi na biyu a Premier

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kammala gasar Premier ta bana a matsayi na biyu ba abu ne da ya fi karfin klub din ba.

A kwanakin nan ne Blackburn ta fitar da Arsenal a gasar cin Kofin Kalubale na Hukumar Kwallon Kafa ta ingila FA, kuma Bayern Munich ta yi nasara a kanta a gasar Zakarun Turai.

Duk da wannan koma bayan, kocin ya yi amanna za su iya samun matsayi na biyu a gasar ta Premier duk da cewa akwai tazarar maki tara tsakaninsu da ta biyu a tebur din Manchester City kuma saura wasanni 11 suka rage a kammala gasar.

Wenger ya ce Manchester City ba ta yi musu tazarar da ba za su iya kamo ta ba, ya ce, ''za ta iya kasance wa gwagwarmaya ce da za a yi har zuwa karshen gasar.''

Nasarar da Arsenal ta samu a kan Aston Villa 2-1 ranar Asabar ita ce ta uku a jere bayan wadda suka samu a kan Sunderland da Stoke.

Duk da wadannan nasarori kungiyar ta kasance ta 5 a bayan City da Chelsea da Tottenham kafin wasan 'yan cikin gida na Landan ta arewa wato Tottenham da Arsenal ranar 3 ga watan Maris.

Manchester United ta daya wadda Arsenal za ta kara da ita a Emirates ranar 28 ga watan Aprilu maki 21 ne tsakaninta da Arsenal din.