Michu ya nemi Laudrup ya tsaya

miguel michu
Image caption Miguel Michu ya gawurta in ji Laudrup

Dan wasan da ya fi kowa cin kwallaye a gasar Kofin Capital One Miguel Michu ya bukaci Micheal Laudrup da ya ci gaba da jagorancin Swansea har gasar Kofin Europa a kakar wasanni ta gaba.

Swansea ta samu gurbi ne a gasar Kofin Europa ta gaba bayan da ta doke Bradford 5-0 ta dauki Kofin Capital One ranar Lahadi.

Laudrup wanda ya rage masa shekara daya a kwantiraginsa da Swansea ya ce zai ci gaba da zama duk da rade-radin da ake yi cewa zai koma Real Madrid ko Chelsea.

Michu wanda kwallon da ya fara cin Bradford a wasan na karshe ita ce kwallonsa ta 19 a bana ya yaba wa Laudrup kan tasirinsa a yadda wasansa ya inganta da na sauran 'yan kungiyar.

Ya ce '' na san wasu kungiyoyin za su neme shi, yana da kyau kuma ya na kokari sosai watakila ya koma wani klub din amma ina fatan zai tsaya.''

A wata kuri'ar jin ra'ayin magoya bayan Real Madrid da aka yi kan wanda su ke so ya gaji Jose Mourinho, Laudrup dan shekara 48 ya samu kashi 72 cikin dari.

Zuwansa Swansea Laudrup ya sayo Michu dan Spaniya daga Rayo Vallecano a 2012 a kan fam miliyan 2.2.

Yanzu kocin ya ce yana ganin darajar Michu ta daga zuwa fam miliyan 30.

Karin bayani