Copa Del Rey: Real Madrid ta casa Barca

real madrid da barcelona
Image caption Real Madrid ta fitar da Barcelona

Real Madrid ta fitar da Barcelona a wasan kusa da na karshe na cin Kofin Copa Del Rey na Spaniya da ci 4-2.

A wasan farko a gidan Real Madrid an tashi ne 1-1, yanzu kuma a ta biyu Madrid ta ci Barca 3-1.

Cristiano Ronaldo ne ya fara cin Barcelona da bugun fanareti a minti 13 da fara wasa, sannan kuma ya kara ta biyu bayan hutun rabin lokaci a minti na 57.

A minti na 68 ne kuma Raphel Varane ya jefa kwallo ta uku a ragar Brcelona.

Sai dai kuma can a minti na 89 ne ana shirin tashi daga wasan Jordi Alba ya samo wa Barcelona kwallo daya.

Real Madrid za ta yi wasan karshe da Sevilla ko Atletico Madrid wadanda su kuma za su yi karawa ta biyu ta wasansu na kusa da na karshe ranar Talata 27 ga watan Fabrairu.