Ronnie zai kare kambunsa na sunuka

Ronnie O'Sullivan
Image caption Ronnie O'Sullivan ya rike kambun wasan sunuka na duniya har sau hudu

Ronnie O'Sullivan ya sanar da cewa zai kare hutunsa, kuma zai komo fagen wasan sunuka domin kare kambunsa na duniya, a watan Aprilu mai zuwa.

Dan wasan mai shekaru 37 ya fice daga kakar wasannin shekarar 2012-13, a watan Nuwambar bara saboda wasu dalilai da suka shafe shi.

An baiwa O'Sullivan nan da 28 ga watan Fabrairu, ya yanke shawara ko zai shiga gasar wasan sunuka ta duniya na wannan shekarar ko kuma a'a.

"Na gaji, sai naga ina bukatar hutu kuma ina ganin lokaci yayi da yakamata na koma kan abin da na saba." A cewar O'Sullivan.

Gasar wasan sunukar na jiran komowar O'Sullivan a hukumance, kuma a matsayinsa na mai rike da kambun wasan, da shi za a bude gasar ta duniya a ranar 20 ga watan Aprilu.

"Dole in koma fagen sunuka ko zan samu nasara ko ba zan samu ba, hakan na nuni da muhimmancin sunuka a rayuwa ta." Inji Ronnie

Inda ya kara da cewa " Aiki na ne kuma na riga na saba da shi, kawai dai ina bukatar in dan samu sararin yin wasu abubuwan ne. Amma dama na kwana da sanin cewa ba zan dade ba zan dawo fagen wasa."