Everton ta doke Oldham da ci 3 da 1

Kulob din Everton
Image caption Akwai rashin tabbas game da matsayin Moyes, saboda ya jinkirta yanke shawara a game da makomarsa har sai karshen kakar wasanni

Kulob din Everton ya dakile burin Oldham a gasar cin kofin FA, bayan ya samu shiga cikin kulob-kulob takwas na karshe ta hanyar lallasa Wigan.

Kevin Mirallas ne ya doka kwallo da ka, kuma ta shiga ragar Oldham, bayan Darron Gibson ya dauko ta.

Nasarar da Everton ta samu ya biyo bayan jajircewa wajen kai hare-hare ga abokan karawarsu, a sulusin karshe na wasa.

Kuma wannan nasarar ita ce ta farko ga Everton, a wasanni biyar na cin kofin.

Hakan dai ya sabunta burin majanan kulob din, David Moyes na daukar kofi a cikin shekaru 11 da yayi yana horar da 'yan wasan kulob din.

Moyes ne ya kai kulob din zuwa zagayen gab da na kusa da na karshe a bara, kuma shi ne ya kai Everton din zuwa zagayen karshe a shekarar 2009.

Sai dai ga manajan kulob din Oldham, Tony Philliskirk wannan ne karon farko da aka lallasa kulob din, a wasanni biyar din da su ka yi, a shekaru biyar da yake jagorancin kulob din.