Djokovic da Federer sun yi gaba a Dubai

djokovic da federer
Image caption Djokovic da Federer na kan hanyar haduwa

Zakarun wasan tennis na duniya Novak Djokovic da Roger Federer sun yi nasarar zuwa wasan kusa da na karshe na gasar Dubai Free Trade.

Zakaran na daya Djokovic ya yi galaba ne a kan dan Italiya Andreas Seppi da maki 6-0 6-3 kuma zai hadu da gwani na hudu a duniya Juan Martin del potro na Argentina.

Shi kuma mai rike da kofin na Dubai zakara na biyu Roger Federer ya samu zuwa wasan kusa da na karshen ne bayan ya buge Nikolay Davydenko da maki 6-2 6-2.

Federer dan Switzerland zai kara ne da Tomas Berdych dan Czech na uku a duniya. A ranar Juma'a ne za a yi wasannin na kusa da karshe.

Djokovic ya na kokarin daukar kofin na hudu ne na gasar ta Dubai a shekaru biyar.