'Ya'yan Pele sun bar wasan kwallo

Andre da Jordan Ayew
Image caption Wa da kanin ba su ce ga lokacin da za su dawo fagen wasan tamaular kasa da kasa ba

Andre da Jordan Ayew sun dakatar da buga wasan kwallo na kasa da kasa, bayan dan rashin jituwa da hukumar kwallon Ghana.

'Yan gida dayan, mai shekaru 23 da kuma 21 na buga wa kulob din Marseille ta Faransa wasa ne.

Kuma sun ce sun dakatar da yin tamaular ne, saboda rikicin dake tsakaninsu da hukumar kwallon Ghana na kara zafi.

An dai cire Andre daga tawagar kwallon kafa ta kasar, da suka je gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika a kasar Afirka ta Kudu, saboda rashin zuwa horo a kan lokaci.

Yayin da kwata-kwata ma ba a sanya dan uwansa Jordan a cikin tawagar ba.

Kuma dukkaninsu sun yarda da cewa maganar tawagar Ghanan ne ya sa suka dakatar da buga kwallo.

'Yan wasan biyu dai 'ya'ya ne ga Abedi Pele Ayew, wanda aka fi sani da Dede, kuma Jordan ne ya rubuta wasiku biyu, da ya aika wa hukumar yana sanar da ita murabus dinsu.

Andre ya ce matsalar da ya samu da masu gudanar da hukumar, ta sa ba zai iya cigaba da buga wasan kwallo ba.

Yayin da shi kuma Jordan yace zai ci gaba da buga kwallo a kulob dinsa, domin ya samu kwarewar da ake bukata wajen sanya shi cikin tawagar kwallon kasar.