Fortune : Man U za ta iya nasara ba Van Persie

robin van persie
Image caption Robin van Persie na murmurewa

Tsohon dan wasan Manchester United Quinton Fortune ya ce yana da kwarin guiwa tsohuwar kungiyar tasa za ta iya samun nasara a kan Real Madrid ko da ba Robin van Persie.

Fortune tsohon dan wasan Afrika ta Kudu mai shekara 35 ya ce rashin Van Persie a wasan ba karamar asara ba ce amma duk da haka nawi ne na sauran 'yan wasan da za su iya ji da shi.

Ya ce yana ganin zamani ne na United yanzu, su na yunwar nasara.

Van Persie dan kasar Netherlands ya ji rauni ne a kuibinsa a lokacin wasan United da QPR ranar Asabar lokacin da ya fada kan wani ramin na'urar daukan hoto.

Kocin Manchester United din Sir Alex Ferguson ya ce ba za a yi karambanin sa shi a wasan da za su yi da Norwhich ba ranar Asabar amma yana ganin zai warware sosai yadda zai iya buga wasansu da Real Madrid karo na biyu.

Kwallaye 23 Van persie ya ci wa United zuwa yanzu a kakar wasansa ta farko da sukahada da 3 a gasar Zakarun Turai.

Shi ma Phil Jones dan wasan baya na United wanda ya taka rawar gani a wasan farko da Madrid din yana kokarin ganin ya murmure daga ciwon idon sawun da ya ji domin ya buga wasan.