Beckham ya zama jakadan kwallon China

David Beckham
Image caption David Beckham ne jakada na musamman a gasar wasannin Olympic na duniya da aka yi a London a shakarar 2012

David Beckham ya zama jakadan kwallo na kasar China, ta haka kasar ke fatan zai ceto mutuncin kwallonta a idanun duniya.

A baya-bayan nan dai gasar zakarun kasar ta fuskanci, abin kunyar nan na sayar da wasanni, ga shi kuma dan wasan nan Didier Drogba ya bar gasar.

Beckham mai shekaru 37 zai hada ayyuka biyu, na wasa a kulob din Faransa, St-German da kuma zama jakadan kasar Sin a fagen wasan tamaula.

A cikin wata sanarwar da ya fitar, Beckham ya bayyana cewa "An yi matukar girmama ni da aka bani wannan mukamin, a wannan lokaci mai muhimmanci a tarihin kwallon kafa na Sin."

Dan wasan dai zai dinga halartar taka ledar gasar zakarun, kuma zai dinga ziyartar kulob-kulob na kasar, domin taimaka wa wajen daga darajar kwallon kafa a tsakanin yara.

Drogba ya taka leda ne a kulob din Shanghai Shenhua na kasar Sin, bayan sanya hannu a kwantiragin shekaru biyu da rabi, a shekarar 2012.

Sai dai a watan Janairun wannan shekarar ya koma kulob din Galatasaray na kasar Turkiyya, a matsayin aro, amma tafiyarsa na cike da cece-kuce.