Klitschko zai kara da Pianeta

wladimir klitschko
Image caption Wladimir Klitschko sau 14 ya na kare kambunsa

Zakaran damben boksin na ajin masu nauyi na duniya Wladimir Klitschko zai kare kambunansa a karawar da zai yi da Francesco Pianeta a watan Mayu.

Klitschco zai kare kambunansa na WBA da IBF da kuma WBO a birnin Mannheim na Jamus ranar 4 ga watan Mayu da Pianetan wanda tsohon abokin atisayensa ne.

Wannan dai shi ne karo na 14 da Klitschko mai shekara 36 dan kasar Ukraine zai kare kambunansa a karo na biyu da yake zaman zakaran dambe na duniya ajin masu nauyi.

Abokin karawar tasa Pianeta wanda dan kasar Italiya ne dake zaune a Jamus a dambensa 29 ba a taba galaba a kansa ba.

Kuma sau daya kawai ya taba yin canjaras.

Pianeta wanda ya ce mutane da dama na yi masa kallon bako a fagen damben boksin ya yi kurarin cewa zai rikita duniyar damben inda zai yi wa Klitschko dukan kawo wuka.

Idan Klitschko ya doke Pianeta dan shekara 28 wata kila zai kara da Alexander Povetkin dan Rasha ko da ike dai a baya dan Rashan ya yi ta kokarin kaucewa karon-batta tsakaninsa da zakaran damben na duniya.

Yayan Wladimir wato Vitali shi ne ke rike da kambun Hukumar damben Duniya ta WBC yayin da David Haye dan Birtaniya da Tyson Fury suke cikin jerin gwarzaye 10 na hukumomin dambe na duniya WBA da IBF da kuma WBO.

Karin bayani