Real Madrid ta fitar da Man United

real madrid da manchester united
Image caption Real Madrid ta shiga wasan gab da na kusa da karshe na zakarun Turai

Manchester United ta sha kashi a hannun Real Madrid a Old Trafford da ci 2-1 da hakan ya sa ta fice daga gasar Zakarun Turai da ci 3-2 gida da waje.

Manchester United ta ci kwallonta ne bayan da Sergio Ramos na Real Madrid ya ci kansu a minti na 48 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Luka Modric ya ramawa Real Madrid a miniti na 66, sannan kuma minti uku tsakani Cristiano Ronaldo ya kara ta biyu.

Jumulla wasa gida da waje Real Madrid 3 Manchester United 2.

Real Madrid ta shiga zagayen wasan gab da na kusa da karshe, United kuwa ta yi waje daga gasar Zakarun Turai.

A daya wasan na Kofin Zakarun Turan Borussia Dortmund ta Jamus a gidanta ta casa Shakhtar Donetsk ta Ukraine 3-0.

Felipe Santana ne ya fara jefa kwallo a ragar bakin a minti na 31 sai Goetze ya kara ta biyu bayan minti 6.

A minti na 59 ne kuma Blaszczykowski ya ci kwallo ta uku.

A karawar kungiyoyin ta farko a Ukraine sun tashi 2-2, da sakamakon na yanzu Borussia Dortmund na da kwallaye 5 yayin da Shakhtar Donetsk ke da 2.

Borussia Dortmund ta shiga jerin kungiyoyi 8 da za su fafata a wasan gab da na kusa da karshe.