Man United za ta yi cinikin Schlupp

jerry schlupp
Image caption Jerry Schlupp na gab da komawa Manchester United

Kungiyar Leicester City na gab da kammala tattaunawa da Manchester United kan sayar da matashin dan wasanta Jeffrey Schlupp

Schlupp mai shekara 20 ya kai sama da wata daya a Old Trafford ana jarraba shi kuma ya buga wasan 'yan kasa da shekara 21 tsakanin United da Liverpool da kuma West Ham a makon da ya wuce.

Schlupp wanda aka haifa a Jamus ya ke bugawa kasarsa Ghana wasa yana wasa ne a gaba amma kuma ya yi wa Leicester wasa a baya ma.

Tsohon kociyan Leicester Sven-Goran Eriksson ya ce bai sani ba ko matashin dan wasan ya kai munzalin tafiya Manchester United wanda ya ce babban ci gaba ne ga dan wasan amma kuma babban rashi ga Leicester.

Karin bayani