Caf : Hayatou zai tsaya zabe ba hamayya

issa hayatou
Image caption Issa Hayatou zai sake yin tazarce

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Afrika Caf Issa Hayatou zai sake tsayawa zabe ba tare da wani ya kalubalance shi ba.

Kotun sauraren kararrakin wasanni wadda ke Switzerland ce ta yi watsi da daukaka kara ta karshe da Jacques Anouma dan Ivory Coast ya yi domin samun damar shiga zaben na ranar Lahadi a Maroko.

Hukuncin na nufin Issa Hayatou wanda ke kan kujerar shugabancin Hukumar ta Caf tun 1987 zai sake tsayawa shi kadai a zaben da za a yi a Marrakech ta Moroko.

A shekarar da ta wuce ne aka haramtawa Anouma yin zabe bayan da hukumar kwallon kafar ta Afrika ta sauya dokokinta.

Sauyin da aka yi a watan Satumba na 2012 ya baiwa mambobin hukumar da ke da damar kada kuri'a ne kawai 'yancin tsayawa takarar shugabanci.

Anouma na cikin 'yan kwamitin zartarwar Caf saboda kasancewarsa daya daga cikin wakilan Afrika a hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA.

Duk da cewa Anouma dan shekara 61 yana halartar taron hukumar Caf amma ba shi da 'yancin yin zabe.

Matakin hana Anouma tsayawa takarar na nufin cewa Issa Hayatou zai ci gaba da shugabancinsa na Caf har shekaru 30.

Wannan shi ne karo na hudu da kotun wasannin ta ke kin amincewa da duk wani kokari na kalubalantar dokokin Caf bayan yunkurin da hukumar kwallon kafa ta Liberia ta yi sau biyu a baya.

Karin bayani