Celtic za ta doke Juventus - Lennon

Manajan kulob din Celtic, Neil Lennon
Image caption 'Yan wasan sun bar Glasgow ba tare da dan wasa Tony Watt ba, saboda raunin da ya samu

Neil Lennon na ganin Celtic za ta doke Juventus, a karawar da za su yi da maraicen ranar Laraba, a zagaye na biyu na gasar cin Kofin Zakarun Turai.

Sai dai bayan Juventus ta lallasa kulob dinsa da ci 3 da nema, a wasan da suka kara a watan Fabrairu, ya amince sai sun yi da gaske.

"Za mu iya cin nasara a taka ledar ranar Laraba, domin abin da mu ke so kenan." Inji Lennon.

Kulob din dai na fatan kaiwa zagayen gaf da na kusa da na karshe a karon farko a gasar.

Inda yake ganin idan za su yi ta kai hari, kamar yadda suka yi a Celtic park, to wasan zai yi kyau.

Sai dai mataimkinsa, Johan Mjallby na da bambancin ra'ayi, inda yake ganin gara 'yan wasan su tsare gida sosai, su kuma bi da Juventus da taka tsantsan.