Manajan Manchester United ya kadu

Manajan Manchester United, Sir Alex Ferguson
Image caption Mataimakin Ferguson, Mike Phelan ya ce sun ji bakin cikin abin da ya faru

Manajan kulob din Manchester United, Sir Alex Ferguson ya kadu matuka, game da fitar da kulob din daga gasar Champions league.

Abin da ya sa ya kasa fuskantar manema labarai, domin yi musu jawabi da aka tashi daga wasan.

Ferguson ya fusata, bayan alkalin wasa Cuneyt Cakir ya kori Nani saboda kalubalantar Alvaro Arbeloa na Real, mintoci 56 da fara wasan.

A wannan lokacin kuma Manchester United ce ke kan gaba a wasan, saboda kwallon da Sergio Ramos ya ciwo mata.

Sai dai bayan korar Nani, Real ta yi amfani da wannan damar, inda ta zura kwallaye biyu a ragar Man U.

Luka Modric da Christiano Ronaldo ne suka zura wa Real Madrid kwallaye a ragar abokiyar karawar tata, a taka ledar da suka yi a filin wasa na Old Trafford.

Nasarar da Real ta samu na ci biyu da daya, ya sanya ta shiga jerin kulob-kulob takwas na gasar, abin da ya sa kuma aka yi waje da Man U.

Mataimakin mai horar da 'yan wasan Man U, Mike Phelan ne ya yi jawabi ga manema labarai, inda ya bayyana cewa ferguson da 'yan wasan na cikin kaduwa.