Juventus ta fitar da Celtic 5-0

juventus celtic
Image caption Juventus ta yi gaba a Kofin Zakarun Turai

Kungiyar Juventus ta yi nasarar zuwa wasan gab da na kusa da karshe na kofin zakarun Turai da ta fitar da Celtic kamar yadda PSG ta yi waje da Valencia.

A karawar da suka yi ranar Laraba Juventus ta ci Celtic din 2-0.

Alessandro Matri ne ya fara jefa kwallon farko a minti na 24, sannan kuma a minti na 65 Fabio Quagliarella ya ci ta biyu.

A karawar farko a gidan Celtic din makwanni uku da suka wuce Juventus din ta ci Celtic 3-0.

A sakamakon wasannin biyu Juventus ta na da ci 5 Celtic ba ko daya.

PSG ta fitar da Valencia

A daya wasan kuma ita ma Paris st Germain ta shiga rukunin wasan gab da na kusa da karshe bayan ta yi galaba a kan Valencia da ci 3-2 a karawa biyu.

A wasansu na ranar Laraba a gidan PSG sun tashi kunnen doki 1-1.

Oliveira ne ya fara ciwa Valencia kwallo a minti na 55 kafin Ezequiel Lavezzi ya rama a minti na 66.

A karawarsu ta farko a watan Fabrairu PSG ta ci Valencia 2-1.

Jumulla wasannin biyu PSG ta yi nasara da ci 3-2.