Uefa za ta hukunta Man United

manchester united real madrid
Image caption Manchester United za ta gamu da hukuncin Uefa

Hukumar kwallon kafa ta Turai ta fara shirye shiryen duba irin hukuncin ladabtarwar da za ta yi wa Manchester United bayan da Real Madrid ta fitar da ita daga gasar Kofin Zakarun Turai da cece-kuce.

Hukumar za ta yanke hukunci ne a kan korar da alkalin wasa ya yi wa Nani ne a wasan da aka fitar da Manchestern da ci 3-2 jumulla wasa gida da waje.

Sannan kuma hukumar za ta yi hukunci kan rashin cika ka'idojin bayan wasa da tawagar Man United din ta yi na kin halartar taron manema labarai a Old Trafford.

Hukumar ta Uefa za ta duba iya yawan wasannin da za ta hana Nani bugawa saboda jan katin na kora da alkalin wasan dan kasar Turkiyya ya bashi a minti na 56.

Alkalin wasan dai ya kori dan wasan ne saboda daga kafarsa da ya yi sama don taro wata kwallo har ta kai sun yi kicibis da Alvaro Arbeloa na Real Madrid da hakan ke zaman tamkar keta ya yi.

Game da taron manema labaran kuwa kocin Man United Sir Alex Ferguson wanda ya fusata saboda hukuncin alkalin wasan na korar Nani ya ki halartar taron manema labarai da shi da sauran 'yan wasansa sai matakimakinsa ne Mike Phelan ya halarta.

A ranar 21 ga watan Maris din nan ne Hukumar ta Uefa ta ce kwamitinta na da'a zai duba batun.

Karin bayani