'Yan sanda sun kama Carlos Tevez

Carlos Tevez
Image caption Carlos Tevez yana taka rawar gani a Man City

BBC ta fahimci cewa 'yan sanda sun kama dan wasan Manchester City Carlos Tevez a garin Cheshire kan zargin tuka mota duk da cewa an kwace lasisinsa na tuki.

Tevez, mai shekaru 29, an tsare shi ne ranar Alhamis da misalin karfe 5:10 agogon GMT a kan titin A538 a Macclesfield.

Amma 'yan sanda sun bayar da belinsa.

An dakatar da dan wasan na Argentina daga tuki tsawon watanni shida a watan Janairu bayan da yaki amsa wasikar da 'yan sanda suka aika masa kan gudu a mota fiye da kima.

Manchester City ta ce ba za ta yi magana a kan batun ba.

Mai magana da yawun 'yan sandan Cheshire ya ce: "Jiya 'yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 29 daga Alderley Edge".

"An kama mutumin ne kan zargin tuka mota duk da cewa an kwace lasisinsa sai dai tuni aka riga aka bayar da belinsa."

Karin bayani