NFF na neman dala 60,000 don wasan Kenya

aminu maigari
Image caption Aminu Migari shugaban NFF dake neman makudan kudade don wasa daya

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta ce tana bukatar dala 60,000 domin shirin wasan neman shiga gasar cin Kofin Duniya tsakanin Najeriya da Kenya.

Hukumar ta ce tana matukar bukatar kudaden domin wasan da za a yi ranar 23 ga watan Maris a birnin Calabar na Najeriyar.

NFF ta kuma ce har yanzu 'yan wasan Najeriyar da suka dauki Kofin Kasashen Afrika a watan Janairu a Afrika ta Kudu suna binta kudaden alawus dinsu.

Hukumar ta yi alkawarin baiwa kowana dan wasa dala 20,000 idan suka yi nasara a kan Burkina Faso a wasan karshe.

Karin bayani