Zaman Rooney a Man United ba tabbas

wayne rooney
Image caption Wayne Rooney na cikin kila-wa-kala a Man united

Da alamu babu tabbas ci gaba da zaman Wayne Rooney a Manchester United kamar yadda rahotanni suke ta yaduwa.

Ko a wasan Manchester United din da Real Madrid ranar Talata sai daga baya aka sa shi a wasan.

Dangane da hakan Jaridu da dama a Ingila ke ganin cewa klub din na shirin rabuwa da dan wasan ne a karshen kakar wasannin nan.

Duk kuwa da cewa saura shekaru biyu a kwantiraginsa da kungiyar.

A watan Oktoba ne na 2010 Rooney ya bayyana cewa yana son barin klub din saboda rashin kokarin nemo kwararrun 'yan wasa abin da ya sa Sir Alex cikin kaka-ni-kayi.

Haka shi ma Sir Alex a taron klub a shrinsu na karawarsu da Real Madrid ya bayyana cewa Rooney zai yi zaman jiran ko-ta-kwana ne a wasan.