Caf : An sake zabar Issa Hayatou

issa hayatou
Image caption Issa Hayatou zai bar Caf a karshen wa'adinsa na bakwai a 2017

An sake zabar shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika Caf Issa Hayatou ba tare da wata hamayya ba.

A shekarar da ta wuce ne aka yi wa dokokin hukumar gyara da hakan ya hana mutumin da ya so ya kalubalanci Hayatoun a shugabancin Jacques Anouma dan Ivory Coast.

Hayatou mai shekaru 66 wanda ya ke kan shugabancin Caf tsawon shekaru 25 zai sauka a karshen wa'adinsa na bakwai a 2017.

An sake zabar Mohamed Raouraoua dan Aljeriya da Amadou Diakite dan Mali da Adoum Djibrine dan Chadi da Magdi Sham El Din na Sudan da kuma Suketu Patel na kasar Seychelles a kwamitin zartawar hukumar.

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Najeriya Aminu Maigari ya fadi a zaben shiga kwamitin zartarwar na Caf.

Anjorin Moucharafou na Jamhuriyar Benin ne ya kayar da shi.

Moucharafou ya yi zaman gidan yari na watanni 6 shekaru 2 da suka wuce a kan almubazzaranci da kudaden daukar nauyin wasanni.

Shi ma Diakite na Mali FIFA ta hana shi shiga harkokin wasanni tsawon shekaru 2 a 2010 a kan zargin sayar da kuri'ar zaben mai karbar bakuncin gasar Kofin Duniya ta 2018 da 2022.