Kofin FA : Man U da Chelsea 2-2

manunited da chelsea
Image caption Fafatawar Man United da Chelsea

Manchester United da Chelsea sun tashi 2-2 a wasan gab da na kusa da karshe na kofin FA.

Minti 5 da fara wasa Hernandez ya fara daga ragar Chelsea, sannan kuma ba jimawa a minti na 11 Rooney ya biyo baya da kwallo ta 2.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a minti na 59 Hazard wanda ya yi canjin Victor Moses ya rama wa Chelsea daya.

Minti tara tsakani ne kuma sai Ramires ya rama ta biyun.

A kusan karshen wasan Chelsea ta kai hare haren da saura kiris da ta samu nasara a kan Man United.

Saboda wasan da Chelsea take da shi na kofin Europa ranar Alhamis ba a tsaida ranar da za a sake karawar tasu ba wadda za a yi a gidan Chelsea.

Yanzu Manchester City wadda ta lallasa Barnsley 5-0 ranar Asabar za ta jira kungiyar da za ta fito a tsakanin Man United da Chelsea ta hadu da ita.

A sauran wasannin Wigan wadda ta ci Everton 3-0 za ta hadu da Millwall ko Blackburn wadanda suka tashi ba ci 0-0, za su sake haduwa ranar Laraba domin fitar da gwani.

Za a yi wasan kusa da karshen ne ranar 13 da 14 na watan Aprilu.