Kofin FA: Millwall da Blackburn za su sake wasa

millwall blackburn
Image caption Millwall da Blackburn sun tashi ba ci

Millwall da Blackburn za su sake fafatawa tsakaninsu a wasan gab da na kusa da karshe na kofin kalubale na FA.

Kungiyoyin da suke rukunin kasa da na Premier za su sake haduwa ne a ranar Laraba saboda tashi canjaras 0-0 da suka yi ranar Lahadi.

Andy Keogh na millwall ne ya kusa ya ci wata kwallo da ka amma ta taba sandar raga.

Su kuma 'yan Blackburn ba su yi wani yunkuri ba sai lokacin da Jordan Rhodesya kai wani hari bayan dawo daga hutun rabin lokaci.

Millwall ta yi ta kai hari amma kusan karshen wasan Blackburn ta farfado inda Josh King ya kai wani hari da kwallon ta doki sandar raga.